Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: A cewar wadannan majiyoyin, matsin lambar da jama'a suka yi, kiraye-kirayen da masu adawa da kawancen Netanyahu da iyalan fursunonin Isra'ila suka yi na cewa Dermer ya sauka daga mukaminsa, su ne manyan abubuwan da suka sa ya yanke wannan shawarar. Yana da kyau a lura cewa gidan talabijin na Channel 7 na Isra'ila ya ba da rahoton karuwar rashin gamsuwar jama'a game da manufofin majalisar ministocin Netanyahu.
Bayan martanin Hamas tayi bisa shirin da Trump ya yi na tsagaita bude wuta
Hamas, ta hanyar bayar da martani mai cike da sharudda ga shirin na Donald Trump mai matakai 20, ta sanar da shirin ta na sakin mutanen da aka yi garkuwa da su da kuma shiga tattaunawa. A sa'i daya kuma, Trump ya yi kira ga Isra'ila da ta gaggauta dakatar da kai harin bam a Gaza.
Sa'i ɗaya kuma Kafofin yada labarai na Ibraniyawa sun ba da rahoto game da rikicin siyasa na cikin gida inda suke kwatanta halin da ake ciki a cikin gwamnati a matsayin tunzurar fushi, damuwa, da rudani. A cewar manazarta, Tel Aviv na sa ran Hamas za ta yi watsi da yarjejeniyar tsagaita bude wuta domin samun hujjar ci gaba da kai hare-hare, amma sabon matakin da Hamas ta dauka ya tayar da jijiyar wuyar ga Isra'ila. Kafofin yada labaran kasashen yammacin duniya sun rawaito cewa matsin lamba ga Isra'ila na dakatar da kai harin ya kara tsananta bayan gargadin da Trump ya yi wa Hamas ("Idan ba ku amince ba zuwa ranar Lahadi jahannama ce jiran ku") sai kuma Hamas tai martani mai kyau ga wannan barazana.
Your Comment